Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na MTV cewa, a jiya ne kungiyar Boko Haram da ke dauke da makamai a Najeriya, ta fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna jagoran kungiyar Abubakar Shekau yana shelanta yin mubaya'a ga jagoran kungiyar Daesh (ISIS) wanda aka fi sani da Abubakar Bagdadi. A cikin faifan bidiyon dai Abubakar Shekau ya yi magana ne da harshen larabci, wanda ake tarjamawa da rubutu turancin Ingilishi da Faransanci, inda yake fadin cewa sun yi mubaya'a ga Ibrahim bin Awad bin Ibrahim Al-hussaini Al-kurshi, wanda aka fi sani da Abubakar Al-bagdadi, jagoran daular muslunci. Tun a cikin watan Yunin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu ne dai ya sanar da kansa a matsayin khalifan musulmi karkashin abin da ya kira daular musulunci a Iraki da Sham. Kungiyar tasa dai ta shahara ne bayan kutsa kai da ta yi a arewacin Iraki a cikin shekara ta dubu biyu da goma sha hudu, tare da kwace wasu yankuna na kasar tare da hadin baki da kuma taimakon wasu kasashe da suke makwftaka da kasar ta Iraki, ya zuwa yanzu dai kungiyar ta kashe dubban fararen hula maza da mata da kanan yara a cikin kasashen yankin. 2953241