Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Al-ra’ayi cewa, Mohammad Al-momini ministan yada labarai kuma kakakin gwamnatin kasar Jordan a lokacin da yake gabatar da jawabi a kwalejin Amir Hussain Bin Abdullah Al-thani, ya jadda muhimmancin irin rawar da kafofin yada labarai na addinin musamman suke takawa wajen wayar da kan sauran al’ummomi dangane da abin da ya kamata su aiwatar.
Ya ci gaba da cewa kafofin yada labarai suna da matukar muhimamnci a cikin kowace al’umma, musamman wanna zamanin da muke rayuwa a cikinsa da duniya ta samu gagarumin ci gaba, kuma a wannan bangaren ma ba a bar kafofin sadarwa a baya ba, domin suna amfani da dukkanin hanyoyin ci gaban zaman domin isar da sakonsu.
Daga cikin muhimamn batutuwan da zaman ya yi dubia aknsu har da yanayn da ake ciki a halin yanzu a yanking abas ta tsakiya da kuma sauran kasashen larabawa, wadanda suke fuskantar matsaloli da tashin hankali, sakamakon haifar da rikicin da aka yi a cikinsu saboda dalilai na siyasa.
A cikin yan kwanakin nan ma kasar ta Jordan ta fuskanci wani aikin ta’addanci inda aka kone daya daga cikin matukan jirgin sama na kasar kurmus a hannun ‘yan ta’adda.
2957633