IQNA

Shugaban Hukumar Leken Asiri Ta CIA Ya Bayyana A Mai Kare Musulunci

23:45 - March 15, 2015
Lambar Labari: 2989485
Bangaren kasa da kasa, John Bernar shugaban hukumar liken asirin kasar Amurka ta CIA ya bayyana a matsayin mai addinin muslunci tare da nisantar da shi daga ayyukan ta’addanci da kuma ‘yan ta’adda.

Kamfanin dillancin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Express Tribune cewa, Bernar ya gargadi dangane da danganta addinin musulunci da kungiyoyi irin su daesh da sauransu, inda y ace bas u wakiltar musulmi balanta addinin musluci.
A cikin bayanin nasa y ace idan za a yi adalci za a ga cewa musulmin duniya  adukkanin kasashe bas u tare da ‘yan ta’adda da kuma ayyukan da suke aikatawa, saboda haka bai kamata wasu su rika fitowa suna cewa addinin muslunci addini ne na ta’addanci ba.
Dangane da hanyoyin da ya kamata a bi wajen fuskatr wadannan mutane kuwa, ya bayyana cewa ya kamata a bi dukkanin hanoyoyi musamman na sadarwar zamani, inda nan yan ta’adda suke jan hankula masu shiga cikinsu domin gano su da kma cafke su.
A cikin ewata zantawa da wani masani dan kasar Amurka ya I a kwanakin baya da tashar PressTV ya bayyana cewa Amurka da ita kanta hukumar CIA su ne suke da hannu kai tsaye wajen samar da kungiyar ‘yan ta’adda ta daesh da sauran kungiyoyi makamantansu a duniya.
Kamar yadda kuma Amurka ta kasance a gaba wajen horar da su da kuma tura su zuwa kasashen da suke gudanar da ayyukan nasu a gabas ta tsakiya musamman.
2986211

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha