IQNA

Shekhul Azhar Ya ce A Shirye Ya ke Ya Tattauna Da Malaman Shi'a A Iraki

23:25 - March 17, 2015
Lambar Labari: 3004314
Bangaren kasa da kasa, bababn malamin cibiyar Azahar ta Masar ya bayyana cewaa a shirye ya shiga tatatunawa tare da mayan malaman mazhabar shi'a a nakasar Iraki domin samun fahimtar juna.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ilaf cewa, a yau Ahmad Tayyib bababn malamin cibiyar Azahar ta Masar ya bayyana cewaa a shirye ya shiga tatatunawa tare da mayan malaman mazhabar shi'a a nakasar Iraki domin samun fahimtar juna da kuma warware matsalolin da suke kunno kai a cikin al'ummar muslumi.

Wannan furuci dai ya zoa  daidai lokacin da malamin yake fuskantar martani da kakkausar suka daga koina cikin kasasheh duniya, bayan day a fito ya zargi sojojin sa kai da suke yaki day an ta'addan Daesh a Iraki, inda ya bayyana cewa yan shi'a ne suke yaki day an sunna.

Tun kafin wannan lokacin Ahmad Tayyib ya fito ya bayyana yan ta'adda daesh da cewa ba musulmi ba ne kuma ya haasta a yake a duk inda aka same su, domin kuwa su a cewarsa suna bata sunan addinin ne, kuma daga bisani ma ya kira su da sunan khawarijawa, amma bayan da suka fara shan kashia  Iraki ya fito ya juya maganarsa.

Saga cikin irin martanin da yake fuskanta hard a kafa masa dalili da abin day a fada kan yan ta'adda wanda shi kansa ya taimaka wajen zaburara da sojin sa kai a Iraki na sunna da shi'a domin yakin yan ta'addan amma kuma ya dawo yana bayyana hakan da cewa yaki ne na shi'a a kan sunna, lamarin da ake kallon cewa yana da alaka da siyasa.

2998942

Abubuwan Da Ya Shafa: Tayyib
captcha