Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na ajib cewa, tun a ranar juamar da ta gabata ce Easley ya sanar da cewa a halin yanzu ya karbi addinin muslunci a matsayin sabuwar hanya tya rayuwa.
Ya sanar da hakan a shafinsa na kafar sadarwa ta yanar gizo ta twitter, inda yake cewa ya shiga muslunci ne sakamakon neman shiruya da yake yi a cikin rayuwarsa, inda daga karshe ya kai ga wannan shiriya da ya ganoo cewa tana cikin addinin muslunci, kamar yadda wannan kalami ya samu ra’ayin mutane 5150 a shafin nasa.
Bisa ga wannan rahoto, wannan dan kwallo na kasar Amurka ya saka hotunansa da ya dauka a cikin wani masallaci tare da wasu musulmi, yayin da yake samun taya murna.