IQNA

An Bude Zaman Taron Karatun Kur'ani Na Duniya A Morocco A Karo Na Biyu

20:04 - March 19, 2015
Lambar Labari: 3012740
Bangaren kasa da kasa, an bude taron karatun kur'ani mai tsarki na kasa da kasa a Morocco tare da halartar makaranta daga kasashen duniya.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, Ahmad Ibadi babban sakataren kungiyar Muhammadiyyah ya bayyana cewa, koyarwar kur'ani a lokacin manzon Allah (SAW) ba ta taikaitu da wasu bangaroro ba kawai na rayuwa, ta hada dukaknin bangarorin rayuwar mutum ne.

Ya ci gaba da cewa mutanen da suke dauke da sakon kur'ani wato wadanda suka zama ahalin kur'ani mai tsarki ta fuskar karatu da bayaninsa ga al'umma, hakika suna da nauyi day a rataya a kansu, na ganin cewa sun yi aiki wanda ke misilta wannan littafi mai tsarki, domin ya zama tarjama ga sauran jama'a.

Haka nan kuma ya kara da cewa, ma'anar nauyin da kuma yadda za su safke hakan shi ne, su san matsayin kur'ani mai tsarki cewa matsayi ne wanda yake kai mutum zuwa ga dukaknin madakkakin matsayi na duniya da lahira, da kuma yadda za a fahimci cewa shi mai dauke da wannan nauyi yana wakiltar lamari mai matukar girma da daukaka.

Yin aiki da abin da ke cikin kr'ani shi ne yin aiki irin na manzon Allah tsira damincin Allah su tababta gare shi, domin kuwa manzo shi ne mai koyar da kyawawan dabiu a cikin ayyyukan rayuwarsa, wadanda dukakninsu kyawawan ayyuka na koyi ga dukkanin dan dama, yin koyi das hi shine tafarkin isa ga sa'adar duniya da ta lahira.

Wasu daga cikin malmai da suka halarci wannan gasa sun bayyana matsayin taron da cewa yana da matukar muhimamnci a dukkanin fuskoki na addini, domin kuwa lamari na dauaka addini da matsayin kur'ani da koyarwarsa  acikin al'ummar musulmi.

3007486

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha