IQNA

Dakunan Karatun A Morocco Wuraren Bayar Da Horo Ne Ga Yara

23:24 - March 22, 2015
Lambar Labari: 3026945
Bangaren kasa da kasa, dakunan karatun kur’ani mai tsarki da ke biranen kasar Morocco sun zama wurin koyar da kananan yara da kuma horar da su a kan ilmomin addini.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-yaoum 24 cewa, an samu ci gaba ta yadda dakunan karatun kur’ani mai tsarki da ke biranen kasar Morocco sun zama wurin koyar da kananan yara da kuma horar da su a kan ilmomin addinin musluncia  fagage daban-daban.
Bayanin ya ci gaba da cewa bisa la’akari da ci gaban da ake samu ta fukoki na ilmi, ya hakan ya sanya malaan kur’ani tare da hadin gwiwa da ma’aikatar ilimi bangaren kula da harkokin karatun kur’ani, suka samar da wani tsari na daban bayan koyar da yara karatun kur’ani mai tsarki, inda akan hada musu da wasu abubuwan na daban.
Daga cikin abubuwan da ake koyar da yara wadanda ba su kai ga shiga makarantun firamare ba, akwai karatu da kuma harda, bayan nan kuma a halin yanzu ana koyarsu da ilmin shari’a ta yadda za su san wasu daga cikin lamurran ibada, kamar alwala da salla da makamathna hakan.
Masu bin lamarin suka ce hakan yana da matukar muhimamnci a dukkanin fuskoki, domin kuwa zai baiwa yara damar tashi da masaniya kan addini, baya ga karatun kur’ani mai tsarki da ake koya musu, ga kuma sauran ilmuka na addini, gami da karatun zamani, wanda hakan zai sanya su ga hanya ta zama cikakun mutane da za su zama abin misali a rayuwarsu.
2957711

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco
captcha