IQNA

Kyamar Musulunci A Amurka Na Shafar 'Yan Sanda Musulmi A Kasar

20:39 - March 25, 2015
Lambar Labari: 3040141
Bangaren kasa da kasa, duk da irin matsaloli da ake fuskanta na nuna wariyar launin fata a Amurka a tsakanin al'ummar kasar musamamn ma wuraren aiki a halin yanzu lamarin har yana shafar 'yan sanda mabiya addinin muslunci a kasar.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Onislam cewa, Mujahid Rashi wani dan sanda ne musulmi a Amurka, ya ce irin matsaloli da ake fuskanta na nuna wariyar launin fata a Amurka a tsakanin al'ummar kasar musamamn ma wuraren aiki a halin yanzu lamarin har yana shafar 'yan sanda mabiya addinin muslunci da suke cikin runsunar yan sanda.

Duk da wannan matsala wani sakamakon jin ra’ayin jama'a ya nuna cewa kimanin kashi sabain da uku cikin dari na wadanda aka saurara sun nuna cewa musulmi suna fuskantar matsi da kuma nuna banbanci da wariya, yayin da wasu kuma kimanin kashi hamsin da biyu suke ganin cewa shi kansa addinin muslunci yana karfafa ayyukan tashin hankali a duniya.

Da dama daga cikin wadanda aka ji ra’ayoyinsu wadanda suka san wasu musulmin kuma suka mu’amala da su sun yi watsi da ra’ayin cewa musulunci shi ne addinin da ke karfafa gwiwa wajen yada ayyukan tashin hankali, domin kuwa sun san musulmi masu son zaman lafiya da kyakkyawar dabia dad an adamtaka.

Shi dai wannan jin ra’ayin jama’a ya hada mutane kimanin dubu daya ne kuma kimanin musulmi miliyan shida zuwa miliyan takwas ne suke rayuwa a cikin fadin kasar Amurka sai dai saboda rashin saninsu hakan ya sanya mafi yawan al’ummar Amurka ba ta da wata masaniya dangane da addinin muslunci.
3040122

Abubuwan Da Ya Shafa: amurka
captcha