IQNA

An sanar Da Sunayen Wadan Da Suka Yi Shahada A yemen Sakamkon Harin saudiyya

23:40 - March 27, 2015
Lambar Labari: 3049249
Bangaren kasa da kasa, an sanar da sunayen mutanen da suka yi shahada sakamakon harin ta’addancin Saudiyya kan al’ummar kasar Yemen da cewa ya kai mutane 25 yayin da adadin ke ci gaba da karuwa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Sharq Alausat cewa, sunayen mutanen da suka yi shahada sakamakon harin ta’addancin Saudiyya kan al’ummar kasar Yemen da cewa ya kai mutane 25 da suka yi shada kuma adadin yana ci gaba da karuwa a kowane lokaci, sakamakon cewa masu kai harin suna ci gaba da yin hakan, daga cikin kasashen ad suka shiga harin bayan kasashen larabawan gabas ta tsakiya, akwai Masar, Jordan, Sudan Morocco da kuma Pakistan.
Jiragen yakin kasar Saudiyya da kawayenta sun ci gaba da kai hare-haren kan wajaje daban-daban na babban birnin kasar Yemen da wasu garuruwa na daban na kasar lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar wani adadi mai yawa na mutanen kasar  da kuma raunata  wasu da daman gaske mafiya yawansu fararen hula.
Rahotannin a wani hari da jiragen saman yakin Saudiyyan suka kai birnin San’ah, babban birnin kasar ta Yemen, harin yayi sanadiyyar mutuwar alal akalla mutane 28 da raunata wasu da dama. Har ila yau kuma jiragen yakin Saudiyyan sun kai hare-hare garin Sa’adah inda a nan ma dai wasu mutane mafiya yawansu fararen hula suka rasu wasu kuma suka sami raunuka.
Kungiyoyi da shugabannin kabilun kasar ta Yemen daban-daban dai sun kirayi al’ummar kasar da su dau makamai don mayar da martani ga wannan wuce gona da iri na Saudiyyan da kawayenta a kan kasar ta Yemen suna masu shan alwashin mayar da martani mai kaushin gaske ga kasar ta Saudiyya.
A daren jiya laraba ce dai kasar Saudiyya da wasu kawayenta na kasashen larabawan Tekun Fasha da suka hada da Qatar, Kuwait, Bahrai, Jordan, Sudan da Masar, bugu da kari kan taimakon gwamnatin Amurka suka kaddamar da hare-hare kan al’ummar Yemen din da sunan kokarin dawo da tsohon shugaban kasar Abd Rabbu Hadi Mansur da ya gudu kan karagar mulki.
3042170

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha