Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Alalam cewa, a lokacin da yake zantawa da tashar talabijin ta CBS ta kasar Amurka, Bashar Assad ya bayyana cewa ‘yan ta’addan daesh sun kara bazuwa ne daga lokacin da Amurka ta fara kai hari da sunan yaki da wannan kungiya ta yan ta’adda.
Ya ci gaba da cewa a kowane lokaci Amurka na kokarin bayyana ma duniya tana cewa mai yaki da kungiyoyin yan ta’adda ce, alhali hakan tantangayar karya ce take shirga ma duniya, domin kawai ta ci gaba da wasa da hankulan al’ummomi kamar yadda ta saba.
Bashar Assad ya ci gaba da cewa yanzu haka akwai yankuna na cikin kasashen Iraki da Syria da yan ta’addan suka mamaye tare da taimakon kasar Amurka da kuma karnukan farautarta daga cikin kasashen larabawa, wadanda a ko da yasuhe suke neman sharri ga wannan al’umma ta musulmi da larabawa.
3059534