IQNA

Kai Hari Kan Yemen Ya Saba Wa Dukkanin Kaidojin Kungiyar Kasashen Larabawa

23:08 - April 01, 2015
Lambar Labari: 3075814
Bangaren kasa da kasa, kungiyoyi 34 na kare hakkin bil adama acikin kasar Yemen da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa sun bayyana hare-haren Saudiyya kan kasar ta Yemen da cewa ya sabawa dukkanin kaidoji da dokoki na kungiyar kasashen larabawa.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar giz na jaridar Misral Yaoum cewa, wasu kungiyoyi na kare hakkin bil adama  acikin kasar Yemen da kuma wasu daga cikin kasashen larabawa sun bayyana harin Saudiyya kan kasar ta Yemen da cewa ya saba wa dukkanin kaidoji da dokoki na kungiyar kasashen larabawa dukkaninsu suka rattaba hannu a kanta.
Wasu bayanai dai sun tabbatar da cewa jiragen saman yakin gidan Sarautar Saudiyya suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan kasar Yemen.
Rahotonni daga kasar ta Yemen suna bayyana cewa jiragen saman yakin gidan Sarautar Saudiyya da ke jagoranta rundunar hadin gwiwar wasu kasashen Larabawa da na ‘yan koransu suna ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan yankunan kasar Yemen musamman garuruwan kasar.

Hare-haren na yau suna zuwa ne kwana guda da jirgin saman yakin Saudiyya ya kai harin wuce gona da iri kan sansanin ‘yan gudun hijiran Yemen a lardin  da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane fararen hula akalla arba’in da biyar tare da jikkata wasu kimanin dari biyu da hamsin  na daban.

Gidan talabijin din Al-Mayadeen mai watsa shirye-shiryensa ta hanyar tauraron dan Adam ya bayyana cewa; Tun daga lokacin da gidan sarautar Saudiyya ya fara jagorantar kai hare-haren wuce gon da iri kan kasar Yemen yau cikon kwanaki na shida, an samu hasarar rayukan mutane fiye da dari daya tare da jikkatan wasu daruruwa na daban.

Ita ma a nata bangaren majalisar dinkin duniya ta fara nuna damuwa a halin yanzu dangane da wannan aikin ta’addancin Saudiyya kan al’ummar kasar Yemen, tare da tabbatar da cewa dole ne a yi bincike kan harin Mazraq.

3072783

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha