Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Saba’a Net cewa, a jiya limaman masallatan juma a kasar Yemen sun bayyana bayar da duk wani taimako ga gidan sarautar Saudiyya da ke kaddamar da hari kan al’ummar kasar da cewa babban hainci ne ga al’ummar kasa baki daya.
A nasu abngare Mayakan kungiyar huthi, sun hallaka sojojin Saudiyya biyu a cikin yankunan kasar ta Yemen da ke kan iyaka da Saudiyyah, tare da jikkata wasu.
Rahotanni sun ce mayakan sun yi musayar wuta mai tsanani da sojojin masarautar Saudiyya a lokacin da suka yi yunkurin tsallaka iyakokin kasar Yemen ta kasa, hakan ya zo ne bayan hallaka wani sojin na Saudiyya guda a ranar Laraba da ta gabata a kan iyakokin kasar ta Yemen.
Majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto da ke cewa akalla mutane dari biya da sha bakwai ne suka rasa rayukansu tun bayan da Saudiyya da masu rufa mata suka fara kaddamar da hare-hare a kan kasar ta Yemen da sunan yaki da 'yan kungiyar Alhuthi, rahoton ya ce akasarin mutanen da suka rasa rayukansu fararen hula mata da kananan yara.
Jiragen yakin na Saudiyya na rufa baya ga mayakan alkaida da yan bindiga da ke mara baya ga shugaban kasar wanda ya tsere zuwa Saudiyya, rahotanni sun tabbatar da cewa Saudiyya tana kaddamar da hare-haren nata ne a kan filayen safka jiragen sama da sauran muhimman wurare na gwamnati da kuma gidajen jama'a, da sunan yaki da 'yan kungiyar huthi.
3083967