Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Akhbar Misr cewa, a jiya cibiyar Azhara ta yi Allawadai da kai harin na kasar kasar Kenya, inda bayan mutuwar wasu dari da hamsin jami’an yan sanda sun tseratar da 600 daga cikin daliban.
A nasu bangaren jagororin kungiyoyin mabiya addinin musulunci a kasar Kenya sun fitar da wani bayani na hadin gwiwa da ke yin Allawadai da kakkausar murya dangane da harin ta'addancin da kungiyar Alshabab ta kai kan wani wurin kwanan daliban Jami'a a yankin Garisa.
A cikin jawabin wanda aka fitar a daren jiya Juma'a, jagororin addinin muslunci na kasar ta Kenya sun bayyana hare-haren da cewa aiki ne na dabbanci, kuma hakan ba shi da wata alaka da addinin muslunci, kuma suna bayar da dukkanin goyon baya ga gwamnatin kasar Kenya wajen daukar dukkanin matakan da suka dace domin yaki da 'yan ta'adda a kasa.
A ranar Alhamis da ta gabata ce mayakan kungiyar Ashabab ta kasar Somalia ta kaddamar da hari kan wurin kwanan daliban jami'ar Garisa a kasar Kenya, inda suka kashe mutane dari da arbain da bakawai , daga cikin wadanda suka rasa rayukansu har da dalibai musulmi.
3090535