IQNA

Ana Sa Ran Masallatan faransa Za Su Ninka Har sau Biyu

18:47 - April 05, 2015
Lambar Labari: 3092635
Bangaren kasa da kasa, babbar majalisar malaman addinin muslunci a kasar Faransa CFCM ta bayyana cewa nan da shekaru biyu masu zuwa akwai yiwuwar masallatan kasar su ninka har sau biyu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Lepoint cewa, Dalil Bubakar shi ne shugaban majalisar malaman addinin muslucin a kasar ta Faransa ya bayyana cewa,a  halin yanzu akwai masallatai 2300, kuma a cewarsa wadanan masallatai za su ninka har sau biyu a cikin shekaru biyu masu zuwa.
Dalil Bubakar ya ci gaba da cewa a halin yanzua kwai musulmi da adadadinsu ya kai miliyan 7 a cikin kasar, kuma wannan adadin masallatai dubu biyu da dari uku ba zai ishe sub a domin gudanar da harkokinsu na addini.
Ya kara da cewa yanzu haka dai suna cikin bin kadun wanann lamari, bisa la’akari da cewa yana bukatar da namijin kokari kafin cimma wannan buri, Dalili Bubakar bai yi Karin haske danagne da hanyoyin da zai bi domin samun kudin gina masallatan ba.

3090479

Abubuwan Da Ya Shafa: France
captcha