IQNA

Al Saud Ba Su Da Alaka Da Musulunci Da Kuma Ahlu Sunnah

23:57 - April 09, 2015
Lambar Labari: 3116035
Bangaren kasa da kasa, George Galawi fitaccen dan siyasa a kasar Birtaniya ya bayyana cewa gidan sarautar Saudiyya ba shi da wata alaka da addinin muslunci balantana ahlusunna.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na  ehlibeytalimleri.com cewa, George Galawi fitaccen dan siyasa a kasar Birtaniya ya bayyana cewa irin munanan ayyukan da gidan sarautar Saudiyya ke aikatawa kan musulmi ba shi da wata alaka da addinin muslunci balantana sunnar manzo.
Ya ci gaba da cewa ina dukkanin karfin Saudiyya yake a lokacin da Haramtacciyar kasar Isra’ila ke lugudan wuta kan musulmin larabawa a yankin zirin Gaza, a lokacin da suke bukatar taimakon dukkanin kasashen musulmi, me yasa ba a ji su ba.
Galawi y ace wananna bin da Saudiyyah take yin a kisan fararen hula a kasar Yemen aiki ne ta ke aiwatarwa na yahudawan sahyuniya, domin tabbatar da cewa an ruguza kasashen musulmi da za su iya taka ma Isra’ila birki, wanda kuma ko shakka babu tarihin Yemen ba boyayyaen lamari ne ba.
Wani rahoto da ma'aikatar lafiya ta kasar Yemen ta fitar ya tababtar da cewa a cikin kwanaki  shga daya da Saudiyya ta kwashe tana lugudan wuta kan biranan kasar Yemen, ta kashe fararen hula dari takwas akasarinsu mata da kananan yara, tare da rusa dubban gidajen jama'a da kaddarorin gwamnati.

Su kuma  wasu daga cikin kungiyoyin kare hakkin bil adama a ciki da wajen kasar suka fara tattara bayanai dangane da laifukan yaki da Saudiyya take tafkawa kan al'ummar Yemen da sunan yaki da kungiyar husi domin gurfanar da mahukuntan na Saudiyya a gaban koton manyan laifukan yaki ta duniya.

3104406

Abubuwan Da Ya Shafa: galawi
captcha