
Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Veto cewa, Shuki Allam wanda shi ne baban mai bayar da fatawa a kasar ya bayyana masu tsatsauran ra’ayi da cewa sun bata sunan alkur’ani da sunnar manzon Allah a idon duniya tare da mayar da kisa da hauka a matsayin addinin da maye gurbin rahama da su.
Malamin ya ci gaba da cewa babbar matsalar da al’ummar musulmi ke fuskanta a halin yanzu ita ce rashin kyakyawan saiti, da kuma karancin ilmin addini, ta yadda wasu masu mummunar akida suka yi amfani da hakan wajen cimma manufarsu ta karkatar da matasan musulmi, tare da saka su cikin mummunar hanyar da sunan addini.
Rashin sani shi ne abin da ke matasa musulmi shiga cikin kungiyoyin yan ta’adda da sunan suna addini, suna kashe musulmi da wand aba muslmi babu gaira babau babu sabat, duk da snan yada addini, wanmda haan ya bar mummunar tasiri dangane da yadda ake kallon addinin muslunci a halin yanzu a idon duniya.
Ya kara da cewa babban aiki ne a gaban malamai masu cikakakiyar masaniya kan addini su mike tsaye domin yakar wannan mummunar akida ta kafirta musulmi tare da halasta jininsa, domin kywa rashin yin hakan babu abin da zai jawowa wannan al’umma illa fitina bakin jini da bata sunanta a duniya, kuma malamai su ne abin tambaya aranar kiyama.
Dangane da abin da ya kamata a mayar da hankali a kansa kuwa., malamin y ace malamai su wayar da kan musulmi musamman matasa hakinanin addinin muslunci na zaman lafiya kamaer yadda manzo y azo da shi a matsayin rahama ga dukkanin talikai.
Ga wadanda ba muulmi ba kuma , dole ne a bayyana musu cewa shi mulunci ba addinin ta’addanci ba ne kamar yadda suka dauka, kuma su ga a hakan a ikace tare da musulmi.
3122373