Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, Ehsan Muhammad Alaridhi, masani malamin jami’a a Iraki ya bayyana cewa, gidan sarautar Saudiyya aiwatar da shirin yahudawan sahyniya kan al’umamr kasar Yemen kamar yadda kowa ya sani.
Rahotanni sun ce fararen hula da dama sun rasa rayukansu a yankin dake yammacin kasar Yemen sanadiyar lugudar wuta da jiragin yakin Al-sa’ud suka yi a yau lahadi. Tashar telbijin Al-masira ta kasar Yemen ta habarta cewa jiragen yakin kasar Saudiya sun yi lugudar wuta kan wani filin wasa da kuma gidajen fararen hular da ke kewayensa a jahar IBB dake yammacin kasar kuma sanadiyar hakan fararen hula da dama sun rasa rayukansu , da dama daga cikinsu Mata ne da kananen yara.
A jiya Assabar ma jiragen yakin masarautar Al-sa’oud sun kai irin wannan hari a filin wasa na garin Yarmuk dake arewacin Sana’a babban birnin kasar , lamarin da ya yi sanadiyar jikkatar fararen hula guda.
Har ila yau jiragen yakin Saudiyar sun yi lukudar wuta a kan gine-ginan gwamnati da ofishoshin jami’an tsaron kasar ta Yemen a yankin Marib, a yankin adan kuwa jiragen ruwan yakin Saudiya ne suka yi lugudar wuta a ma’ajiyar alkama da kuma gine-ginan gwamnati dake wannan gari.
A gefe guda kuma jiragen yakin na masarautar Al-sa’oud suka hare-hare kan gidajen fararen hula a yankin Sa’adah dake yammacin kasar, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar fararen hula tare da jikkata wani adadi mai yawa daga cikinsu.
Jiragen yakin masarautar Saudiyyah sun yi lugudan wuta kan kauyen Al-jund da ke cikin lardin Ta'iz a Rewacin kasar Yemen da asubahin yau, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar fararen hula da dama.
Rahotanni daga kasar ta Yemen sun ce jiragen yakin na Al Saud sun fara kaddamar da hare-haren ne a lokacin da ake shirin gudanar da sallar asubahin yau, mahukunta alardin sun ce har zuwa safiyar motocin daukar gawawwaki da wadanda suka samu raunuka suna ta kai komo a yankin, domin kwashe wadanda harin ya kashe ko ya jikkata, akasarin mutane da suka rasa rayukansu dai mata ne da kananan yara
.
A kan iyakokin kasar ta Yemen da Saudiyyah kuwa, rahotanni sun ce an yi musayar wuta tsakanin mayakan Ansarullah (Al-huthi) da kuma sojojin masarautar Al Saud, inda mayakan na Alhuthi suka hallaka uku daga cikin manyan jami'an sojin masarautar ta Al Sau.
3107665