IQNA

Neman Hukunta Mabiya Mazhabar Shi’a A Masar Bisa Tuhuma Maras Asasi

23:30 - April 13, 2015
Lambar Labari: 3138521
Bangaren kasa da kasa, Walid Isma’il mai Magana da yawun kungiyar salafiyyah a kasar Masar ya bayyana mabiya mazhabar shi’a da cewa suna matukar hadari a kasar kuma dole a gurfanar da su.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawwabah News cewa, Walid Isma’il mai kula da harkokin yada labarai da kuma magana da yawun kungiyar salafiyyah a kasar Masar ya bayyana mabiya mazhabar shi’a da cewa su ne babban hadari da ke fuskantar kasar Masar baki daya.
A kan hakan wannan dan salafiyya ya bukaci mahukuntan Masar da su bi diddigin duk inda yan shi’a suke a kame su baki daya  akai su a gaban kotu domin a hakunta su, bisa hujjar cewa suna dauke da akida mai matukar hadari wadda za ta iya kawo tashin hankali a kasar.
Ya ci gaba da cewa hadarin yan shi’a ya fi hadarin yan ta’adda da suke da alaka da kungiyar Ikhwanul musulmin, wanda a cewarsa hakan zai bayyana a nan gaba idan kuma ba  adauki matakan da suka dace ba a cewarsa wajen yaki da yan shi’a a kasar, to kuwa lokaci zai kure na yin haka.
Mabiya mazhabar shi’a a Masar dai na fuskantar matsaloli na tsangwama daga mabiya tafarki kafirta musulmi, wanda yake samun karfi da gindin zama a tsakanin al’ummar masar a wannan zamani.
3133126

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha