IQNA

An Buga Tare Da Raba Wani Karamin Littafi Kan Hanhuwar Fatima (SA) A Kenya

22:15 - April 14, 2015
Lambar Labari: 3144967
Bangaren kasa da kasa, karamin ofishin jakadancin jamhuriyar muslunci ta Iran a birnin Nairobi an kasar Kenya ya buga tare da yada wani karamin littafi kan haihuwar Sayyidah Fatima Zahra (SA)

Kamfanin dillancin labaran Iqna daga bangarensa na Afirka ya habarta cewa, an gudanar da wani taro a ofishin jakadancin Iran a birnin Nairobi na kasar Kenya kan ranar haihuwar Fatima Zahra (SA) tare da raba karamin littafi da aka rbuta kan rayuwarta.
Haka nan kuma an raba wanan littafi a sauran yankuna na kasar Kenya ga mabiya addinin muslunci, da hakan ya hada da masallacin Ja’afari, tsibirin Lamo, Nakoro da kuma babban dakin karatu na yankin Mombasa da kuma Malindi domin amfanin musulmi.
Bayanin ya ci gaba da cewa wanann karamin littafi an rubuta shi ne dangane da rayuwarta (SA) da kuma hadisan manzon Alalh (SAW) da suka yi Magana a kanta da kuma matsayinta a cikin addini, gami da muhimman abubuwan da za a iya koya daga rayuwarta (SA) a wannan zamani a tsakanin al’ummar musulmi.
Domin kara yada bayanai dangane da matsayinta madaukaki a tsakanin al’ummar wanann yanki na nahiyar Afirka, an buga kwafin wannan littafi har guda 400 da aka tarjama a cikin harshen turancin english domin ci raba shi ga jama’a da suka fahimtar harshen turanci.
3139529

Abubuwan Da Ya Shafa: kenya
captcha