IQNA

Kin Amincewar Mutanen Yemen Da Wahabiyanci Na Daga Cikin Dalilan Kai Musu Hari

23:42 - April 15, 2015
Lambar Labari: 3151460
Bangaren kasa da kasa, tsawon shekaru da dama al’ummar kasar Yemen suna rayuwa tare da juna ba tare da wata matsala ba amma wahabiyawan Saudiyya sun yi kokarin cusa akidarsu a kasar kuma jama’a suka ki amincewa wanda hakan ya jawo hari a kansu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa a zantawa da Sadeqgh Maglis daya daga cikin mambobin kungiyar Ansarullah a kasar Yemen ya bayyana cewa, Saudiyya tana huce haushinta kan al’ummar Yemen saboda tsawon shekaru da dama al’ummar kasar Yemen suna rayuwa tare da juna ba tare da wata matsala ba amma wahabiyawan Saudiyya sun yi kokarin kawo akidarsu mutane suka yi watsi da ita.
Larabawan yankin tekun fasha karkashin jagorancin Saudiyya da kuma kasashen yammacin turai, sun yi fatali da wani daftarin kudiri wa kwamitin tsaron majalisar dinkin dinkin duniya, da ke neman a dakatar da bude wuta a kasar Yemen, domin bayar da dama ga masu ayyukan agaji su taimaka ma fararen hula da yaki ya rutsa da su. 

Ka'awar  jakadiyyar kasar jodan a majalisar dinkin duniya, ita ce ta wakilci kasashen larabawan yankin tekun fasha guda biyar da suke cikin kawancen da ke kaddamar da hari kan al'ummar Yemen karkashin jagorancin Saudiyya, ta ce ba za su amince da daftarin kudirin rasha ba, domin kuwa kasashen larabawan yankin tekun fasha suna da nasu daftarin kudirin da za su gabatar, yayin da shi kuma mataimakin jakadan kasar turai  a majalisar dinkin duniya ya dora alhakin dukaknin abin da ke faruwa a Yemen kaco kaf kan kungiyar Ansarullah.

Daftrain kudirin kasashen larabawan yankin tekun fasha dai wanda kasashen turai ke mara wa baya, bai amince da batun dakatar da bude wuta a kasar Yemen ba, kuma ya bukaci kwamitin ya tsaro ya yi Allawadai da kungiyar Al-huthi tare da haramta bayar da makamai ga kungiyar da kuma rundunar sojin Yemen, yayin da ita kuma Rasha take ganin idan za a yi hakan to dole ne a haramta bayar da makaman har ga 'yan alkaida da sauran 'yan bindiga da ke mara baya ga shugaban kasar ta Yemen da ya tsere zuwa Saudiyyah, tare da mayar da hankali ga batun dakatar da bude wuta, da kuma warware matsalar ta hanyar tattaunawa tsakanin dukkanin bangaroi a kasar ta Yemen, shawarar da Saudiyya da kasashen turai suka ki amincewa da ita.

A nata bangaren rundunar sojin kasar Yemen ta sanar da cewa ta samu tarin makamai da jiragen masarautar Al Saud suka jefa ma 'yan alkaida a yankin Lahaj da ke kudancin kasar, rahotanni sun  habarta cewa, a jiya manyan jiragen daukar kaya na sojojin saudiyya sun safke makamai masu tarin yawa a wani wuri a cikin lardin Lajad da ke kudancin kasar ta Yemen ga 'yan alkaida, amma kafi su isa wurin sojojin kasar ta Yemen tare da sauran sojojin sa kai sun riga su isa, inda suka kwashe makaman baki daya.
Rahotanni sun ce mutane takwas  suka rasa rayukansu da suka hada da kanan yara a lugudan wutar da jiragen yakin masarautar Al Saud da ke rike da madafun iko a Saudiya suka yi kan al'ummar Sa'ad a arewacin kasar, tare da lalata babban filin wasanni na birnin.

3128986

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha