Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Alahad cewa, a cikin wani bayani da ba a saba jin irinsa ba da kungiyar Hizbullah ta fitar, ta soki gwamnatin Saudiyya dangane irin hankoron da take yin a ganin ta haddasa rikici tsakanin musulmi da kuma saka musu gaba da Iran wadda ta tsaya kai da fatan domin ganin an warware matsalolin da suke addabar musulmi.
Shugaban kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon yayi kakkausar suka ga harin wuce gona da irin da kasar Saudiyya take jagoranta kan kasar Yemen inda yayi kiran da a gaggauta dakatar da wannan harin kamar yadda kuma yace al’ummar Yemen din suna da hakkin kare kansu kuma ma za su yi hakan.
Ya bayyana hakan ne a wani jawabi da yayi a daren jiya ta gidan talabijin din al-Manar mallakar kungiyar ta Hizbullah inda ya ce manufar wannan harin ita ce kokarin Saudiyyan na dawo da ikonta a kasar Yemen din sabanin abin da gwamantin Saudiyyan ta sanar na cewa ta fara kai harin ne don kasar Yemen ta zamanto barazana ga tsaron kasar.
A wani bangare na jawabin nasa ya soki kasar Saudiyyan a matsayin kanwa uwar gamin dukkanin yake-yake da ayyukan ta’addancin da ke faruwa a kasashen larabawa musamman a kasashen Iraki da iriya ta hanyar goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda da suke ci gaba da zubar da jinin al’ummomin wadannan kasashen.
Haka nan kuma ya kirayi al’ummar kasashen larabawa da na musulmi da su goyi bayan al’ummar Yemen da suke fuskantar wannan wuce gona da iri na kasar Saudiyya bisa goyon bayan kasar Amurka inda ya ce ko shakka babu al’ummar kasar Yemen za su yi nasara kan wannan sabon makircin na Saudiyya kamar yadda suka yi a baya.
Gwamnatin wahabiyawan saudiyya dai it ace kan gaba wajen kaddamar da yaki kan al’ummar kasar Yemen, wadanda ba su gani ba, tare da daukar sojojin haya na wasu gwamnatocin domin taimakama ta da kuma kokarin mayar da rikicin na banbancin mazhaba.
Bayanin y ace abin da Saudiya ke yi yana da matukar hadari a kan al’ummar musulmi da larabawa, kuma ya zama wajibi ne dukkanin musulmi su taka mata burki kan wanann babban shiri mai hadari da take aiwatarwa.