IQNA

Al’ummar Yemen Sun Yi Zanga-Zangar La’antar Saudiyyah Kan Hare-Harenta A Kansu

23:17 - April 19, 2015
Lambar Labari: 3175674
Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Yemen suna ci gaba da fitowa a birane daban-daba na kasar domin nuna rashin amincewarsu da hare-haren ta’addanci da Saudiyya ke kaddamarwa a kansu.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na tashar Al-alam cewa, dubun dubatan al’ummar kasar kasar Yemen a garuruwa daban-daban na kasar ne suka fito kan tituna don gudanar da wata gagarumar zanga-zangar Allah wadai da ci gaba da hare-haren wuce gona da iri da Saudiyya take kai wa kasar bugu da kari kan tofin Allah tsine da takunkumin da majalisar dinkin duniya  ta sanya wa ‘yan kungiyar Ansarullah.
Rahotanni sun ce masu zanga-zangar wadanda suka fito a garuruwan Sana’a da sauransu suna rera taken Allah wadai da kasar Saudiyya da murka saboda hare-haren wuce gona da irin da suke ci gaba da kai musu suna masu cewa ko da wasa al’ummar Yemen ba za su taba mika kai ba.

Har ila yau masu zanga-zangar sun bayyana kasar Saudiyyan a matsayin kawar mai kashe kananan yara da mata; haka nan kuma sun yi Allah wadai da majalisar dinkin duniya  saboda kudurin da kwamitin tsaron na majalisar ya fitar inda ya sanya takunkumin kan dakarun Ansarullah din da suke fada da sojojin Saudiyya da ‘yan korensu da suke cikin kasar ta Yemen.

A shekaran jiya ne dai kwamitin tsaron majalisar dinkin duniya  ya amince da wani kuduri da kasashen larabawan Tekun Fasha suka gabatar masa inda ya sanya takunkumin sayen makamai da sauransu kan kungiyar Ansarullah din, lamarin da ake ganinsa a matsayin goyon bayan bangare guda cikin rikicin na Yemen.

3172326

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha