IQNA

An Soki lamirin masar saboda Saka Lamurran Siyasa A Cikin Harkokin Kur'ani

23:54 - April 22, 2015
Lambar Labari: 3194132
Bangaren kasa da kasa, Hazim Abdulazim daya daga cikin masu fafutuka a kasar masar yay i kakakusar suka ga ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar dangane da saka batutuwa na siyasa a cikin harkar da ta shafi kur'ani.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Misr Press cewa, Hazim Abdulazim daya daga cikin masu fafutuka a kasar masar acikin wani bayaninsa  ya yi kakakusar suka ga ma'aikatar kula da harkokin addini ta kasar masar din, kan saka batutuwa na siyasa a cikin harkar da ta shafi karatu da gasar ta kur'ani mai tsarki a kasar.
Dangane da kin gayyatar wasu kasashe da suka hada da kasar Qatar, ya bayyana cewa shin kasar ta Qatar ba ta da yancin ta halarci wanann gasa ne ta kur'ani saboda tana da matsalar siyasa da gwamnati da ke kan karagar mulki a halin yanzu a kasar ta Masar?
A cikin kwanakin da suka gabata ne Muhammad Abdulwazzaq kakakin ma’aikatar harkokin addini a kasar Masar ya bayyana cewa, batutuwa na siyasa ne babban dalilin da yasa ba a gayyaci jamhuriyar muslunci ta Iran zuwa gasar kur’ani ta kasar masar karo na ashirin da biyu, kamar yadda kuma ba a gayyaci wasu kasashen ba da suka hada da Turkiya da Qatar zuwa wannan gasa ba, saboda matsalolin da ke tsakaninsu da Masar.
Duk da irin wannan mataki da kasar Masar take dauka kan jamhuriyar muslunci  a nata bangaren  tana bayar da muhimamnci matuka wajen gayyatar dukkanin kasashen musulmi a tarukanta na gasar kur’ani da hakan ya hada da wakilan kasar Masar, domin kuwa batu na kur’ani bai dace a saka batun siyasa a cikinsa ba
3184390

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha