IQNA

UNESCO Ta Bukaci Isra’ila Da Ta Dakatar Da Duk Wani Aikin Barna A Quds

23:43 - April 23, 2015
Lambar Labari: 3199228
Bangaren kasa da kasa, hukumar bunkasa harkokin ilimi da tarihi tarihi da al’adu ta majalisar dinkin duniya UNESCO ta kirayi haramtacciyar kasar Isra’ila da ta kawo karshen gina ramuka abirnin Quds da take yi.

Kamfanin dilalncin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Albawaba cewa, UNESCO hukumar bunkasa harkokin ilimi da tarihi tarihi da al’adu ta majalisar dinkin duniya ta kirayi haramtacciyar kasar Isra’ila da ta kawo karshen gina ramuka da take ci gaba da yi a cikin birnin Quds, da nufin rusa masallacin mai alfarma.
Tun a cikin sheka ta 1981 zuw shekara ta 1982 ne hokumar ta saka birnin Quds a cikin jerin muhimman wurare na tarihi na duniya, kasantuwarsa daya daga cikin dadadun wurare masu tarihi na duniya da ba za a manta da sub a, musamman ma tarihin annabawa da kuma wurare da suke da laka da su da massalci mai alfarma da ke birnin..
Yahudawan sahyuniya msu tsatsauran ra’ayi da ke samun cikaken goyon bayan daga haramatcciyar kasar Isra’ila da kuma wasu kungiyoyin yahudawa na kasashen turai, sun kudir aniyar rusa masallacin Quds ta hanyar tuna ramuka  akarkashin gininsa, ta yadda zai rufta da kansa, domin raba musulmi da daya daga cikin muhimamn wurarensu masu tsarki.
3191015

Abubuwan Da Ya Shafa: unesco
captcha