IQNA

Kungiyar Kasashen Musulmi Ta Yi Kiran zama Dangane Da Rikicin Kasar Yemen

23:48 - April 25, 2015
Lambar Labari: 3206878
Bangaren kasa da kasa, kungiyar kasashen msuulmi ta yi kiran gudanar da zaman gagagwa danagne da harin wuce gona da irin da masarautar saudiyawa ke kaiwa kan al’ummar kasar Yemen.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Yemen News cewa, a zaman da kungiyar kasashen msuulmi ta yi kiran gudanar da zaman gagagwa danagne da harin wuce gona da irin da masarautar saudiyawa ke kaiwa kan al’ummar kasar Yemen bayan da jami’an kasar ta Yemen suka bayar da shawar hakan.
A nasa bangaren wanda ya jagoranci sallah juma’a a baban birnin jamhuriyar musulunci ya bayyana cewa, harin wuce gona da iri da saudiya gami da magoya bayanta ke kaiwa a kasar yemen kaskanci ga kasashen duniya baki daya.
Ya ci gaba da bayyana cewa masarautar Al’sa’oud tare da goyon bayan wasu kasashen larabawa kalkashin amincewar kasashe masu karfi a duniya na ci gaba da kai hare-haren wuce gona da iri kan al’ummar kasar Yemen ba tare da la’akari ba da dokokin kasa da kasa sun rusa zaman lafiyar yankin baki daya, kuma wannan babban kasakanci ne ga kasahsen musulmi da na duniya baki daya
Yayin dake ishara kan faduwar magabatan kasashen da suke kiran kansu da magabatan musulmi  a siyasance, ya ce magabatan Al-sa’oud na kiran kansu da sunan masu hidima ga haramai  yayin da suke keta alhurmar musulmi da kuma kisan Al’ummar musulmi a kasar Yemen.

Haka nan kuma ya kara da cewa ya zuwa yanzu babu wata nasara da saudiya da cimma a kan manufofin da ya sanya ta kai wannan hari kuma nan gaba ma ba za ta ci nasara ba da yardarm a  al’ummar yemen sun samawa kasar su ‘yan ci daga milkin mallaka ne saboda hadin kai da kuma koyi da juyin juya halin misulinci.

3202399

Abubuwan Da Ya Shafa: oic
captcha