IQNA

An Gudanar Da Tattanawa Dangane Da Batun Magance Kyamar Musulmi A Canada

22:20 - April 28, 2015
Lambar Labari: 3226336
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wani taron tattaunawa dangane da batun matlar kyamar muslmi da ke gudana a birnin Winsdor na kasar Canada tsakanin bangarorin musulmi da na gwamnati.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, a jiya Muhammad Nur daya daga cikin mabiya addinin muslunci da suka harci taron ya bayyana cewa, manufarsu ita ce tattaunawa dangane da batun matlar kyamar muslmi da ke gudana a wasu yankuna na kasar, kuma daliban jami’a musu;lmi ne suka shirya taron.
Haka nan daya daga cikin jagororin mabiya addinin muslunc a garin Windrose na kasar Canada ya bayyana cewa, sun fara bayar da horo ga musulmi domin sanin yadda za su kare addininsu daga mabarnata.
Ya kara da cewa an dauki wanann mataki bisa la'akari da yadda masu tsananin adawa da addinin muslunci suke ci gaba da kokarin ganin sun bata sunan wannan addini a kasar, ta hanayar bayyana shi a matsayin addinin ta'addanci da jahilci da dabbanci.
Masu yin hakan suna masu kafa dalili da ayyuakan wasu jahilan musulmi masu ta'addanci da sunan muslunci a wasu kasashe mabiya addinin muslunci an fuskantar matsaloli a kasar daga masu tsananin kiyayya da musulunci musamman a birnin.
3223182

Abubuwan Da Ya Shafa: canada
captcha