IQNA

‘Yan Takfiriyyah Sun Yi Watsi Da Kiran Kur’ani Na Rashin Tilasci A Addini

20:59 - April 29, 2015
Lambar Labari: 3231792
Bangaren kasa da kasa, Rashid Gannushi jagoran kungiyar Nahda a kasar Tunisia ya bayyana cewa ‘yan takfiriyya sun yi watsi da kiran kur’ani mai tsarki na cewa babu tilascia cikin addini wanda kuma hakan shi ne dalilin da yasa suka fada cikin barna.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Youm Sabe cewa, Rashid Gannushi ya fitar da wani bayani da ke cewa, masu bin akidar kafirta musulmi takfiriyya sun yi watsi da kiran kur’ani mai tsarki da kuma koyarwarsa kan cewa babu tilasci a cikin addini.
Wanann lamari shi ne babbana bin da ya jefa wadannan mutane a cikin fangima da shirme, ta yadda har ma suka shiga kashe mutane da sunan suna neman su shigar da su a cikin addini da karfin bindiga da kisa, maimakon yin amfani da hanyoyi na hikima da rahama irin tadadini muslunci.
Ya zo a cikin kur’ani mai tsarki a cikin aya ta 256 surat Bakara cewa, babu tilasci a cikin addini, sai dai su ko dai bas u san da haka ba ko kuma sun yi watsi da wannan abin da ayar take yin bayani a kasansa ga muusmi.
Haka nan kuma a cikin Surat Nahl aya ta 125 an yi kira ga musulmi da su yi kira zuwa ga ubangiji ta hanyoyi na hikima da kuma wa’azi kyakkyawa, maimakon yin amfani da tashin hankali da tsorata jama’a.
Hakan nan kuma yazo a cikin surat kafirun cewa kafirai suna da addininsu musulmi suna da nasu, wanda abin da masu akidar kafirta musulmi suke babu abin da zai haifarv illa korar mutane daga addini.
3228625

Abubuwan Da Ya Shafa: tunis
captcha