IQNA

Daesh Ta Haramta Koyon Ilmin Sanin Lamurran Tarihin Al’ummomi

20:03 - May 02, 2015
Lambar Labari: 3244098
Bangaren kasa da kasa, kungiyar yan ta’addan daesh ta haramta koyon ilimin sanin harkokin tarihin al’ummomi da kayan tarihinsu da ke komawa zuwa zamun da suka gabata.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-slam cewa, Aiman Tamimi wani babban kungiyar ta yan ta’addan ya bayyana cewa, babbar manufarsu ta yin hakan ita ce domin kada mutane su koma a nan gaba suna bautar gumaka.

Ya kara da cewa baya ga haramta koyon ilimin sanin tarhin al’ummomi da kuma kayayyakin tarihinsu da ke komawa zuwa ga karnonin da suka gabata, kungiyar ta haramta mallakar hotel a dukkanin yankunan da take da iko da su.

Tun kafin wannan lokacin dai hukumar da ke kula da ayyukan yawon shakatawa a kasar Iraki ta bayyana cewa, idsan ba a yi hanzari wajen daukar matakan kare wuraren tarihi na kasar yadda ya kamata ba, to kuwa wannna kungiyar ta yan ta’addan za ta rusa su baki daya.

3241064

Abubuwan Da Ya Shafa: daesh
captcha