IQNA

Al’ummar Yemen Sun Gangamin La’antar Saudiyya A gaban Ginin Majasar Dinkin Duniya

20:05 - May 02, 2015
Lambar Labari: 3244099
Bangaren kasa da kasa, al’ummar kasar Yemen sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a biranin sana’a da ma wasu biranan kasar domin la’antar gidana sarautar Al Saud gami da Amurka.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarat cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tahsar Amayadeen cewa, jama’a dubban daruruwa a Yemen sun gudanar da jerin gwano a biranin sana’a da ma wasu biranan kasar domin la’antar gidana Saudiyya da yan koranta dangane da hare-haremn da suke ci gaba da kaiwa a kansu.
Rahotani daga kasar Yemen na cewa jiragen yakin gidan sarautar Al Saud tare da taimakon Amurka na ci gaba da kddamr da hare-haren kan birane da kauyuka makonni biyar a jere, da sunan yaki da 'yan kungiyar huthi.

 

Yanzu haka dai rhotanni sun ce da jijjifin safiyar yau jiragen yakin na Saudiyya sun kai hari a kan wata unguwa a cikin birnin Aden, inda inda wasu mutane 5 iyalan gida guda da suka hada da wata mata da diyarta budurwa suka rasa rayukansu, yayin wasu gine-gine suka rushe baki daya a cikin unguar, har yanzu ana ci gaba da tona buraguzai domin ceto wadanda suka rage da rai da kuma ton gawwwakin wadanda suka rasa rayukansu.

Hare-haren na Saudiyya kan al'ummar kasar Yemen na ci gaba da tsananta ne a cikin wannan wata na Rajab mai alfarma, daya daga cikin watanni uku da Allah ya haramta yaki a cikinsu, duk kuwa da cewa masarautar ta sanar da kawo karshen yakin nata kan al'ummar Yemen a makon da ya gabata.

A jiya Litinin dubban daruruwan jama'a sun fito kan titunan birnin San'a fadar mulkin kasar ta Yemen suna la'antar Amurka da masaurat Al Saud, sakamakon hare-haren da suke kaddamarwa a kansu.

Kasashen duniya dai sun yi gum da bakunansu dangane da wannan aiki na ta’addanci da jikokin Saud Saud suke kaddamarwa kan al’ummar kasar ta Yemen, wanda hakan ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da suka hada da mata da kanan yara.

3240054

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha