IQNA

An Fara Gudanar Da Gasar Karatu Da Tajwidin Kur’ani A kasar Tunisia

23:51 - May 03, 2015
Lambar Labari: 3250569
Bangaren kasa da kasa, an fara gudanar da gasar karatu da tajwidin kur’ani mai tsarki karo na 14 a masallacin Zaituna da ke cikin birnin Tunis.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Almasdar cew, an fara gudanar da gasar ta karatu da tajwidin kur’anine tare da halartar wakilai daga kasashe 23 na duniya.
Abdulsattar Badar mataimakin ministan da ke kula da harkokin addini a kasar ta Tunisia ya bayyana cewa a kowane bangare akwai mahalarta 20 da za su kara da juna a cikin.
Ya kara da cewa akwai alakalai da za su alkalanci a dukkanin bangarorin gasar su 11, shida daga cikin yan kasar ta Tunisia ne sauran biyar kuma sun zo daga kasashen duniya daban-daban.
Abdulsattar Badar ya kara da cewaa  kowane bangare da ake gudanar da gasar za a fitar da mutane 10 a matsayin wadanda suka lashe a bangaren da suka kara da junansu, kuma su ne za su isa zuwa mataki nag aba.
Ya ci gaba da cewa wannan gasar an agudanar da ita  akaro na goma sha hudu Kenan a kowace shekara  ajere, kuma da yardarm za a ci gaba da yin hakan domin habbaka lamurra da suka danganci kur’ani mai tsarki a kasar.
Daga karshe za a bayar da kyautuka na musamman ga dukaknin wadanda suka nuna kwazoa  dukanin bangarorin da ake gudanar da gasar, wanda kuma shugaban kasar ne da kansa zai dauki nauyin mika kyautuka ga wadanda suka nuna kwazo.
3248352

Abubuwan Da Ya Shafa: tunis
captcha