Kamfanin dillancin labaran AFP ya habarta cewa, Raimon Zafilin Imbolo ministan harkokin cikin kasar ta Congo ya bayyana cewa kafa dokar hana mata saka hijabi cikakke da ya hada da nikabi saboda dalilai na tsaro da suka shafi kasar a cikin wadannan lokuta.
Haji Abdullah Jibril Buwaika shugaban majalisar musulmin kasar ta Congo ya bayyana cewa, matakin da gwamnatin kasar ta dauka ya yi daidai, domin wasu daga cikin matan kasar da ba musulmi ba ne ana mafani da su ta hanyoyi na Mafia domin gudana r da wasu ayyuka na ta’addanci,a akan za su fuskanci wannan kalu bale ne kawai ta hanyar hana saka nikabi ga mata baki daya akasar a wurare na hada-hadar jama’a.
Ya ci gaba da cewa mata musulmi za su ci gaba da yin amfani da nikabi a gidajensu ko kuma a wurare na tarukan addini idan suna bukata, amma a ba a cikin jama’a ba da kuma sauran wuraren ayyuka na gwamnati, domin hakan zai bayar da dama r daukar matakan tsaro yadda ya kamata.
Akwai musulmi kimanin 800,000 a cikin jamhuriyar dimokradiyyar Congo, amma kasha 90 cikin dari bay an asalin kasar ba ne, sun zo ne daga kasashen yammavin nahiyar Afirka, sai kuma wasu daga cikin kasashen larabawa, yayin da kuma kimanin kasha 10 cikin dari su ne yan asalin kasar, kasha 90 cikin daro na mutanen Congo dai mabiya addinin kirista ne.
An dauki wannan matakin ne domin kara tabbatar da tsaro, da kuma kauce ma abin da yake faruwa na Boko Haram a Najeriya, inda yan matan kan saka hijabi kuma su tayar da bam.