Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na Saba net cewa, hukumar Bada Agaji ta duniya ta Red Cross ta yi gargadi akan rushewar harkokin lafiya a kasar Yemen. Hukumar bada agaji ta Red Cross da ke Kasar Yemen ta fitar da bayani a yau asabar da a ciki ta ce; Da akwai hatsari mai girma dangane da halin kiwon lafiya kuma yana ci gaba da karuwa akodayaushe.
Bayanin ya ci gaba da cea; Tun daga lokacin da Kasar Saudiyya ta fara kai hari a cikin kasar Yemen, asibitocin kasar sun cika da wadanda su ka jikkata sanadiyyar jikkata, kuma likitoci da masu jiyya da dama sun fice daga cikin kasar. Mutane da dama sun rasa rayukansu saboda jikkatar da su ka yi da kuma rashin samun magani.
Hare-haren da Saudiyyar ta ke kai wa a cikin kasar ta Yemen dai suna kashe da jikkata fararen hula ne da kuma lalata muhimman cibiyoyin gwamnati.
Jiragen saman yakin Saudiyya sun kai hare-hare kan filin jirgin saman birnin Sana’a fadar mulkin kasar Yeman tare da lalata hanyar da jirage ke tafiya a kai domin tashi ko sauka da nufin hana jirgin saman kasar Iran mai dauke da kayayyakin jin kai sauka a filin jirgin saman birnin.
Kakakin rundunar kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin kasar Saudiyya da suke kai hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yeman ya bayyana cewar sun yi luguden wuta kan filin jirgin saman birnin Sana’a ne bayan da jirgin saman kasar Iran ya ki bada hadin kai ga rundunar kawancen Larabawa bayan da suka bukaci ya koma inda ya fito.
Majiyar gwamnatin Yeman ta sanar da cewar jirgin saman kasar ta jamhuriyar muslunci yana dauke ne da kayayyakin jin kai ne ga al’ummar Yeman, kuma akwai bukatar jirgin ya kwashi tarin mutanen da suka samu raunuka zuwa kasar Iran domin yi musu jinya.
Tuni dai kungiyar bada agajin gaggawa ta kasa da kasa Red Cross ta sanar da cewar kasar Yeman ta kama hanyar shiga cikin bala’i da masifar rayuwa.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadi kan irin mummunan halin da al’ummar Yeman ke fuskanta sakamakon hare-haren wuce gona da iri kan kasar.
Majiyar Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewar hare-haren wuce gona da iri da jiragen saman yakin kawancen kasashen Larabawa karkashin jagorancin Saudiyya ke kai wa kan kasar Yeman suna ci gaba da wurga rayuwar al’ummar kasar cikin mummunan hali lamarin da ke bukatar hanzarta aikewa da tallafin gaggawa zuwa kasar.
Majiyar ta kara da cewa; A halin yanzu haka fiye da mutane miliyan bakawai ne suke cikin mawuyacin hali a Yeman sakamakon hare-haren wuce gona da iri kan kasar, inda al’umma ke bukatar tallafin gaggawa musamman a fuskar kiwo lafiya.