IQNA

Kalaman Batunci ga Muslunci Na Dan Siyasar Birtaniya Sun Bar Baya Da Kura

23:57 - May 11, 2015
Lambar Labari: 3288735
Bangaren kasa da kasa, Dan Siyasar kasar Birtaniya mai tsananin kiyayya da musulmi Paul Golding ya bayyana a gaban jami'an 'yan sandan kasar, domin amsa tambayoyi kan wasu kalaman batunci da ya yi kan addinin muslunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Birmingham Mail cewa, Golding ya jagoranci wani dan kwarkwaryan maci a garin Daley domin nuna rashin amincewa da gina masallaci a garin, wanda mutane kimanin 150 daga cikin magoya bayansa ne tare da shi a wurin.

 

Bayanin ya ci gaba da cewa tun kafin wannan lokacin mutumin ya sha alwashin daukar dukaknin matakan da ya ga sun dace domin hana gina masallaci a garin nasu, kamar yadda ya sake jadda ahakan a wurin da ya jagoranci gangamin.

Ya ce matukar dai yana da rai kuma yana lumfashi ba zai taba bari a gina masallaci a wurin ba, sai dai duk abin da zai faru ya faru da shi da magoya bayansa da ke da iri tunaninsa  agarin masu kiyayya da muslunci.

 

Haka nan kuma bai tsaya  anan ba Golding ya ci gaba da yin kalamai na batunci ga addinin muslunci da kuma dkkanin muslmi har da manzon rahma (SAW).

Amjad Reza daya daga cikin jami’ai masu kula da babban masallacin Dadly ya bayyana cewa wannan shi ne karon farko da dan siyasar ke yin batunci kan muslunci da kuma manzon Allah (SAW) ba, ya sha yin hakan, kuma ba a boye ba da nufin tunzura su su tayar da hankali.

 

Sai dai suna daukar matakai na kauce ma dukkanin abin da zai kawo sabani a tsakaninsu da sauran mutane, kamar yadda muslunci ya koyar da su.

3288643

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha