IQNA

Kungiyar Hizbullah ta Allawadai Da Kaiwa Tashar Al-masiriyya Ta Kasar Yemen Hari

22:02 - May 12, 2015
Lambar Labari: 3294191
Bangaren kasa da kasa, kungiyar gwagwarmayar muslunci ta Hizbullah ta yi kakkausar dangane da harin kawancen Saudiyyah da Amurka ya kai kan tashar talabijin ta Al-masiriyyah ta kasar Yemen tare da bayyana hakan a matsayin keta huromin dokokin duniya.

Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-manar cewa, a cikin wani bayani da kungiyar Hizbullah ta fitar a jiya, ta yi kakkausar dangane da harin kawancen Saudiyyah da Amurka ya kai kan tashar talabijin ta Al-masiriyyah ta kasar Yemen tare da bayyana hakan a matsayin keta huromin dokokin kasa da kasa, da kuma kokarin rufe gaskiyar abin da yake faruwa  akasar.
A cikin wani jawabi da ya gabatar dangane da abin da ke faruwa na harin ta’addancin Saudiyya kan kasar Yemen babban sakataren kungiyar Hizbullahi ta  ya yi kira ga duniya da ta yi aiki da hakkin da ya rataya a wuyarta na ganin an kawo karshen hare-haren wuce gona da iri kan kasar Yeman.
A jawabin da ya gabatar babban sakataren kungiyar Hizbullahi  ya tabo tarin matsalolin da suke addabar kasashen yankin gabas ta tsakaniya, inda ya tabo hare-haren wuce gona da iri da kasar Saudiyya ke jagoranta kan kasar Yeman tare da yin amfani da makamai da dokokin kasa da kasa suka hana amfani da su musamman harba bama-bamai masu ‘ya’ya, rusa duk wasu abubuwa masu amfani a kasar ta Yeman da hana aikewa da kayayyakin jin kai.

Har ila yau ya tabo batun mummunar aniyar Amurka ta raba kasashen yankin gabas ta tsakiya, kamar yadda a halin yanzu Majalisar Dokokin kasar Amurka ta bijiro da batun raba kasar Iraki kashi uku a kan tubali na mazhaba da kabilanci, kuma wannan mummunar aniya tana hakon kasashen iriya, Yeman da sauran kasashen Larabawa.

Ita wannan ta ta Almasiriyyah mallakin kungiyar Anasarullah ce, da ke bayyana hakikanin abin da yake faruwa a kasar ta Yemen wanda sauran mutane ba su sani ba, musamamn ma ganin cewa kafofin yada labaran kasashen yammacin turai da nalarabawa ba fadin gaskiyar ta’addanci da Saudiyya ke yia  kasar ta Yemen.

3290781

Abubuwan Da Ya Shafa: hizbullah
captcha