IQNA

Mahukuntan saudiyya Sun Dage Zartar Hukuncin Kisa Kan Ayatollah Nimir

23:40 - May 13, 2015
Lambar Labari: 3299706
Bangaren kasa da kasa, wata majiya daga yankin Alawamiyyah na gabacin kasar Saudiyyah ta tababtar da mahukuntan kasar sun dakatar da zartar da hukuncin kisa kan malamin addini na kasar Ayatollah Baqer Namir.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa, mahukuntan kasar sun dakatar da zartar da hukuncin kisa kan malamin addini na kasar Ayatollah Baqer Namir har sai abin da hali ya yi.

Majiyar ta ce hakan ya tabbata ne bayan da mahkuntan na masarautar Saudiyya suka tuntubi yalan shehin malamin, tare da tabbatar musu da cewa an dage batun zartar da hukunci, amma dai yana nan ba janye shi ba, sai ba a san ranar zartar da shi ba.

Mahuntan masarautar dai sun baiwa iyalan Ayatollah Nimir damar ziyartarsa a ramar 28 ga wannan wata na Mayu a gidan Kason da ake tsare da shi, domin samun damar ganawa da shi.

Kafin wannan lokacin dai wasu kafofin yada labarai sun bayar da rahotannin cewa an zatar da hukuncin kisa kan shehin malamin, kafin daga bisani ta bayyana cewa babu gaskiya a cikin rahotannin.

Kasashen duniya gami da kungiyoyin kare hakkin bil adama na duniya dai sun ca kan masarautar ta Saudiyya da kada ta yi gigin kashe malamin idan tana son zaman lafiya.

3295252

Abubuwan Da Ya Shafa: saudiyya
captcha