IQNA

Masu Kyamar Musulunci Sun Hana Gudanar Da Baje kolin Littafan Musulunci A Belgium

23:43 - May 13, 2015
Lambar Labari: 3299707
Bangaren kasa da kasa, wasu masu tsananin kyamar addinin muslunci a kasar Belgium sun suna rashin amincewarsu da gudanar da baje kolin littafan muslunci a garin Antorpon na kasar.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa,a  jiya wasu yan tsirarun masu tsananin kyamar addinin muslunci a kasar Belgium sun suna rashin amincewarsu da gudanar da baje kolin littafan muslunci a garin Antorpon da ke arewacin kasar wanda aka saba gudanarwa.

Bayanin ya ci gaba da cewa wanann dai bas hi ne karon farko da ake gudanmar da irin baje kolin ba, domin kuwa an kwashi tsawon shekaru ana gudanar da shi a kowace shekara ba tare da wata matsala ba, ta yadda har ma wasu da ba musulmi suna halartar domin gane ma idanunsu irin littafan da ake bajewa.

Masu tsakanin kiyayya da muslunci da kuma baki yan kasashen ketare da suke a kasar sun fara daukar mataki ne daga wanann shekara, amma duk da hakan dai an ci gaba da gudanarwa, kuma mahukunta suna sane da hakan, kuma sun dauki dukkanin matakan bayar da kariya ga taron.

Brnin dai na daga cikin birane da musulmi suke da karanci, amma duk da haka ba su daina gudanar da harkokinsu, duk kuwa da cewa musulmin da suke a birnin Brussel babban birnin sun fi su yawa da kuma gudanar da harkokin cikin yanci ba tare da fuskantar wata tsangwama daga wani bangare ba.

3297446

Abubuwan Da Ya Shafa: belgium
captcha