IQNA

Kwalejin Kasa A Birtaniya Ta Kori Wani Malami Saboda Cin Zarafin Musulunci

23:53 - May 15, 2015
Lambar Labari: 3304011
Bangaren kasa da kasa, An korin wani malami a babbar kwalejin kasar Birtaniya saboda cin zarafin addinin muslunci da yake yia kowane lokaci a cikin makarantar.


Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na On Islam cewa, Kwalejin kasa ta Birtaniya (National College) ta kori wani malami kuma Pastor mai suna Robert West, saboda kalaman batunci da yake yi kan addinin muslunci a gaban daliban kwalejin, da suka hada mabiya addinai daban-daban.

Bayanin ya ci gaba da cewa daukar wannan mataki ya zo bayan ja masa kunai a lokuta da dama amma kuma bai bari ba, ya ci gaba da cin zarafin musulmi, lamarin da ya sanya dalibai musulmi da ma wadanda ba musulmi suka ci gaba da kai koke ga mahukuntan matakarantar.

Daga karshe dai an dauki matakin korarsa domin hakan ya zama darasi ga masu yin hakan, ko kuma masu tunanin cin zarafin wani addini  a cikin kwalejin a nan gaba.

Robert West dai ba shi da wata alaka da wata majami’a  akasar ta Birtaniya, amma  acikin shekara ta 2006 ya mayar da wani dan karamin gidansa a matsayin wurin da yake yi wa’azin kiristanci.

3300724

Abubuwan Da Ya Shafa: birtaniya
captcha