IQNA

An Gudanar Da Taron Tuanawa Da Shadar Iamm Musa Kazem (AS) A Australia

23:57 - May 15, 2015
Lambar Labari: 3304013
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da taron tunawa da zagayowar lokacin shahadar Imam Musa Kazem (AS) a kasar Australia.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na banagaren yada labaransa cewa, an gudanar da taron ne a na Tunawa da Iamm kazem (AS) a cibiyar Ja’afariyya da ke birnin Adlyid na kasar.

 

Bayanin ya ci gaba da cewa an gudanar da karatun Du’a Komail a wurin, kafin daga bisani Hojjatol Eslam Golam Ali Haidari ya gabatar da jawabi danagne da matsayin Imam kazem (AS) da kuma irin gdunmawar da ya bayar wajen shiryar da al’umma da kuma ilmantar da ita.

Haka nan kuma an gabatar da jawabai kan matsayin shugabanni daga iyalan gidan manzo (AS) da kuma wajabcin yin riko da koyarwarsu kamar yadda amnazon Alalh bisa umarnin Allah madaukiakin sarki ya yi umarni.

 

Wannan dai na daga cikin ayyukan da wannan cibiya take gudanarwa domin yada koyarwarwar iyalan gidan manzo (AS) a tsakanin muslumi kasar.
3303864

Abubuwan Da Ya Shafa: australia
captcha