Kamfanin dilalncin labaran iqn aya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar talabijin ta Al-alam cewa, wani adadi mai yawa na ‘yan kasar Saudiyya da masu goya musu baya sun gudanar da wata zanga-zanga a ofishin jakadancin kasar da ke birnin London don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsarewa da kuma azabtar da ‘yan adawa da gwamnatin kasar take yi.
Rahotanni daga birnin London din sun ce masu zanga-zangar dai suna Allah wadai ne da abin da suka kira mulkin kama-karya da kuma ci gaba da tsare masu adawa da mulkin mulukiyya na Saudiyyan.
Masu zanga-zangar har ila yau sun yi Allah wadai da ci gaba da tsare babban malamin Shi’a na kasar Sheikh Nimr Baqir al-Nimr da gwamnatin Saudiyyan take ci gaba da yi suna masu zargin gwamnatin da kirkirar karya kansa da kuma hana shi samun kulawa ta likitanci.
Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama na kasa da kasa da dama suna ci gaba da sukar kasar Saudiyyan saboda take hakkokin al’ummar kasar da take ci gaba da yi.
Kasar Saudiyyah ta kai makura acikin yan lokutan nan wajen nuna tsananin kiyayya da gaba ga mabiya tafarkin manzon Allah a ciki da wajen kasar, da nufin dushe hasken tafarkin iyalan gidan manzo.
Kungiyoyi kare hakkin bila adama a ikin kasashen larabawa da kuma sauran kasashen duniya suna ci gaba da yin kira da a gagaguta sakin shehin malamin da ake tsare da shi a Sadiyyah saboda ra’ayinsa na neman sauyi.