Kamfanin dilalncin labaran Iqn aya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Naba’a cewa, Kungiyar kare hakin bil adama ta duniya Amnesty International ta ce hukuncin kisan da kotun Masar ta yankewa Hanbareren shugaban Muhamad Morsi ba sabawa dokokin kasa da kasa.
Jim kadan bayan yanke hukuncin kisa kan hambararen shugaban kasar Masar kungiyar kare hakin bil-adama ta duniya ta fitar da sanarwa inda ta ce wannan hukunci ya sabawa dokokin kasa da kasa sannan ta bukaci gwamnatin ta Masar da ta saki hanbararen shugaban kasar ko kuma a sake yi masa shara’a ta adalci a wata kotu ta fararen hula.
A nasa waje jigo a kungiyar ‘yan musulmi ya ce hukuncin kisan da kotun hukunma manyan laifuka ta kasar ta yankewa zababen shugaban Masar na farko ta hanyar democradiya kamar hukuncin kisa ne aka yankewa juyin juya halin kasar ta Masar.
Deraj ya kara da cewa wannan hukuncin da kotun ta yanke siyasa ce sannan ya bukaci ‘yan kasar ta Masar da su fito kan tituna da dandalin juyin milki domin kalubalantar Gwamnatin ta Masar.
A dazu dazun nan ne dai wata Kotun birnin Alkahira da take shari’ar hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi da wasu mukarrabansa na kungiyar ‘yan uwa musulmi ta ta yanke hukuncin kisa kan hambararren shugaban kasar Muhammad Morsi kan laifin wurga tsaron kasar ta Masar cikin hatsari ta hanyar sanar da kasar bayanan sirrin kasa da kuma gudu daga gidan kurkuku a shekara ta 2013.
Har ila yau kotun ta yanke hukunci kisa kan mukarraban hambararren shugaban su dari kan samunsu da laifin fasa gidan kurkuku a lokacin tarzomar juyin juya halin da aka yi a kasar wacce ta yi sanadiyar kifar da gwamnatin Husni Mubarak a shekara ta dubu da sha daya.
3304216