IQNA

An Fara Wani Horo Na Hardar Kur’ani Ga Dalibai Yan Australia A Qom

23:51 - May 19, 2015
Lambar Labari: 3305571
Bangaren kasa da kasa, an fara aiwatar wani sabon shiri na bayar da horo kan hardar kur’ani mai tsarki ga daliban addini yan kasar Australia da ska karatu a birnin Qom.

Kmafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na QAF cewa, wannan horo da aka fara ana gudanar da shi ne  a hubbaren Sayyih Ma’asumah SA) a birnin, wanda Sayyd Mahdi Hussain mahardacin kur’ani mai tsarki yake jagoranta.

 

Wannan shiri yan adaga cikin irin ayyaukan da ake gudanmarwa a lokutan da ake kusantar watan azumin Ramadan mai alfarma, kuma wannan horo zai dauki tsawon wata guda ana gudanar da shi, tare da halartar daliban da suke bukatar samun horon kamar dai yadda aka bayyana.

Ya ci gaba da cewa baya ga karatu da kuma hardar kur’ani mai tsarki, akwai wasu karatuka da za a gudanar da nufin kara yada ilmin Ahlul bait (AS) ga daliban, haka nan kuma shugaban bangaren kula da ayyukan hubbaren na Sayyid ma’asuma (SA) Sheikh Mahdi Bagdadi ya bayyana cewa wannan horo yan ada matkar muhimamnci da tasiri wajen kara yada ilmin iyalan gidan amnzo.

 

Hubbare Sayyida Ma’asuma (SA) dai wata bababr cibiyar ta yada ilmomin iyalan gidan manzo da kuma samun tarbiyar ruhi, inda malamai a tsawon tarihi ske girmama wannan wuri da kuma bas hi mahimamnci ta fuskar yin amfani da si domin wannan manufa.

3305478

Abubuwan Da Ya Shafa: iran
captcha