IQNA

An Zabi Ahmad Nu’aina A Matsayin Shugaban Kungiyar Makaranta Ku’ani Ta Larabawa

23:52 - May 22, 2015
Lambar Labari: 3306376
Bangaren kasa da kasa, kungiyar al’umu da kuma majalisun dokokin kasashen larabawa karkashin jagorancin Abdulaziz Abdullah tazabi Ahmad Ahmad Nu’aina a matsayin shugaban kungiyar makaranta kur’ani larabawa.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na jaridar Yaom Sabe cewa, Abdulaziz Abdullah ya bayyana cewa wanann kungiya ta makaranta kr’ani ta kasashen larabawa za ta zama mai mambobi daga kasashen larabawa daban-daban da suka taka muhimmiyar rawa a wannan bagire.

Ya ci gaba da cewa bababr manufar kafa wannan kngiyar dai ita ce karfafa harkar karatun kur’ani mai tsarki a cikin kasashen larabawa, tare da kare manfofin addini ta hanyar bayyana koyarwar kur’ania  tsakanin larabawa musulmi da wadanda ba musulomi, domin kowa ya kara samun masaniya dangane da koyarwar kur’ani mai tsarki.

Abdulaziz Abdullah ya kara da cewa a cikin yan kwanaki masu zuwa za afara gudanar da wani shiri na bayar da horo, domin tura makaranta daga kasashen larabawa daban-daban zuwa kasashen duniya a cikin watan Ramadan, domin koyar da mutane karratun kur’ani.

3306287

Abubuwan Da Ya Shafa: masar
captcha