Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Sadal Balad cewa Ahmad Tayyib Sheikhul Azahar ya fitar da wani bayani da a cikinsa ya yi gargadi dangane da barazanar yan ta’addan Daesh na rusa wuraren tarihi na Syria da cewa; rusa wuraren tarihi ko kuma sace kayan tarihi na al’umma ko sayar da su haramun ne a shari’ar addinin muslunci.
Ahmad Tayyib yace yana kira ga dukkanin al’umma da su bayar da dukkanin goyon bayansu da taimakonsu domin kare wuraren tarihi na kasar Syria musamman ma yankin Tadmur wanda ya fada hannun yan ta’addan Daesh, wanda kuma a halin yanzu yake fuskantar rusawa daga gare su.
Ya kara da cewa abin da wadannan mutane suke yi bas hi da wata alaka da addinin muslunci ko kuma wani addini na dan adam, domin kuwa abin da suke yi wanda kuma a haka akidarsu take babu yan adamtaka acikinsa, balanata Imani ko wani mai alaka da musulunci.
A makon da ya gabata ne dai yan ta’addansuka kwace iko da garin na Tadmur a kasar Syria, kuma sun fara rusa wasu dag acikin dadaddun abubuwa na tarihi da ke a wannan bagere mai tsawon tarihi a kasar ta Syria.
A nata bangaren hukumar UNESCO ta bayyana cewa rsa wannan wuri zai zama wata babbar asara ce ga tarihin dan adam da ba za a iya yin ramuwarta ba.
3307792