Kamfanin dillancin labaran Iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo cewa, majalisar hadin kan musulmi da kungiyoyin yan shi’a da dama sun gudanar da jerin gwano domin nuna rashin aincewa da ayyukan ta’addancin da ke lashe rayukan jama’a a garin Kuita a lokacin janazar wadanda suka yi shahada sakamakon harin ta’addanci da aka kai.
A lokacin janazar an gudanar da jawabai da ke yin kakakusar suka da yin Allawadai da ayykan ta’addanci, da kuma kasashen da suke daukar nauyin wadannan ayyuka domin haddasa rikicin banbancin mazhaba tsakanin al’ummar musulmi, tare da rarraba kansu.
Haka nan kuma masu jerin gwanon sun dora alhakin abin da ke faruwa kan wasu kungiyoyin ta’addanci guda biyu da suke kai hare-hare kan yan shi’a a garin na Kuita da ma wasu biranen kasar ta Pakistan, haka nan kuma sun kirayi mahukunta da su safke nauyin da ya rataya a kansu kan wannan batu.
Mabiya mazhabar iyalan gidan manzo musamman a garin na Kuita na kasar Pakistan sun jima suna fuskantar irin wadannan matsaloli na ta’addanci daga masu nuna musu gaba a kasar, duk kuwa da cewa hakan bai sanya su sun dauki matakan ramuwar gayya ba, maimakon hakan sun fifita bin hanyoyi na hikima domin fuskantar lamarin.
3308189