IQNA

An Soki Lamirin Azahar Dangne Da Harin Ta’addanci Kan Yemen

20:44 - May 28, 2015
Lambar Labari: 3308733
Bangaren kasa da kasa, shugaban majalisar malaman addinin ta kasar Yemen ya aike da wata wasika zuwa ga tsohon mai bayar da fatawa na kasar Masar yana mai sukar Azahar kan shiru da ta yi kan harin Saudiyyah Yemen.


Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Al-ahd cewa, Sheikh Shasuddin Sharafuddin shugaban majalisar malaman addinin ta kasar Yemen ya aike da wata wasika zuwa ga tsohon mai bayar da fatawa na kasar Masar Sheikh Ali Juma’a yana mai sukar matakain da cibiyar Azhar kan shiru da ta yi kan harin Saudiyyah a kan musulmin kasar Yemen marassa kariya.

Ya ci gaba da cewa a cikin wasikar abin takaici ne yadda kasar Masar ta zama yar amshin shata ga Saudiyyah, kuma tabi sahunta wajen kashe yanuwanta musulmi a kasar Yemen, domin dadata wa Amurka da Isra’ila, hakan yasa suka dage wajen cutar da yan uwansu.

Shamsuddini Sharafuddin ya ce suna jiran su ga malaman Masar sun yi aiki da abin da suka sani na daga ilimi, maimaikon zama yan amshin shata wajen yi wa makiya musulunci aiki da sunan addini da fatawa ta kare manufar makiya muslunci domin farantawa shugabanni da sarakuna rai.

Shugaban majlaisar malaman kasar ta Yemen ya gargadi kasar Masar da cewa, taimakawa ayyukan ta’addanci domin rusa wata kasa ba zai taba barin ita ma kasar ta Masar ba, domin kuwa lokacinta yana zuwa, kuma yadda aka rusa wasu kasashen musulmi da na larabawa wanann shiri ba zai tsallake masar ba domin ta taimaka ma masu aiwatar da shi, saboda haka a yi hattara.

Tun a ranar 26 ga watan Maris na wannan shekara ne dai Saudiyya ta fara kaddamar da hare-hare kan al’ummar musulmi na kasar Yemen, tare da kashe dubbai da kuma jikkata su, yayin da kimanin mutane dubu100 na kasar ta Yemen suka zama yan gudun hijira.

3308649

Abubuwan Da Ya Shafa: yemen
captcha