IQNA

22:45 - May 29, 2015
Lambar Labari: 3308859
Bangaren kasa da kasa, mahukunta ayankin Kebek na kasar Canada sun fara daukar matakai na yaki da ayyukan ta’addanci ta hanayar hada karfi tare da limaman masallatai.


Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Radio-Canada cewa gwamnatin lardin Kebek na kasar Canada sun fara daukar matakai na yaki da ayyukan ta’addanci da kuma hana matasa shiga wannan mummunar hanyar tare da hada karfi tare da limaman masallatai na mabiya addinin muslunci a lardin baki daya.

Theriault shi ne gwamnan lardin, ya bayyana cewa suna samun nasara matuka sakamakon hadin kai da malamai gami da limamai suke bayarwa wajen fuskantar samari matasa masu saka kansu kan turbar ta’addanci da suna addinin muslunci.

Y ace za su ci gaba da bin wannan hanya domin malamai su safke nauyin da ya rataya a kansu na fadakar da matasa su gane cewa ayyukan ta’addanci bas u da wata alaka da addinin muslunci, kuma abin da suke yi kisan kai ne babban laifi a mahangar addinin muslunci.

A cikin makon da ya gabata ne dai jami’an tsaro suka kame wasu matasa suna nufin tafiya zuwa kasar Turkiya da nufin shiga Syria, domin hadewa da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar da suke kashe jama’a da sunan muslunci.

3308569

Abubuwan Da Ya Shafa: Canada
Suna:
Adireshin Email:
* Ra'ayinka:
* captcha: