IQNA

Kokarin Dawo Da Batun palastinu A Cikin Littafan Koyarwa A Tunisia

22:49 - May 29, 2015
Lambar Labari: 3308861
Bangaren kasa da kasa, wasu daga cikin ‘yan siyasa da masu rajin kare hakkin bil adama a Tunisia na hankoron ganin an dawo da batun palastinu a cikin littafan koyarwa a kasar.


Kafanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Al-alam cewa, maganar Palastinu a cikin littafan koyarwa a Tunia an manta da ita tun lokacin shugabancinZainul Abidin, amma yanzu wasu daga cikin ‘yan siyasa da masu rajin kare hakkin bil adama a kasar na hankoron ganin an dawo da batun palastinu a cikin littafan koyarwa a Tunisia.

Aiman Alawi ya mamba a majalisar dookin kasar daga bangaren masu rajin kare hakkokin larabawa ya bayyana cewa suna hankoronganin an raya a batun palastinu a tsakanin yara yan makaranta a kasar, maimakon ci gaba da yanayin da aka bari a baya.

Murad Yakubi malamin jami’a masanin tarihi ya bayyana cewa, ba za su bar batun palastinu ya zama tarihi a kasar suba, za su ci gaba da yin dukkanin abin da ya kamata domin da wannan batu mai matukar muhimmanci a tsakanin al’ummar musulmi da larabawa.

Muhammad kamal Almagribi, dan gwagwarmaya ne kan ganin an kare hakkokin palastinawa da kuma tabbatar da cewa ba kulla alaka da haramtacciyar kasar Isr’ailaba, ya bayyana cewa suna nan daram a kan bakansu na kin amincewa da haramtacciyar kasar yahdawa.

3308791

Abubuwan Da Ya Shafa: tunis
captcha