Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na OIC cewa, kungiyar za ta gudanar da wannan taron ne tare da halartar wakilai na kasashe da dama da mambobi a kungiyar wadanda suke da masaniya kan harkoki na kare hakkin bil adama.
Za a gabatar da bayanai a taron da za su mayar da hankali kan batun dokokin kungiyar da suka hana yin amfani da sunan addini wajen tunzura jama’a ko nuna kyama ga wasu mutane ko addini ko akida, tare da haifar da fitintinu tsakanin al’umma.
A cikin shekara ta 2011 babban sakataren kungiyar, tare da ministan harkokin wajen kasar Amurka, da babban jami’in kula da harkokin siyasar wajen tarayyar turai, gami da wasu daga cikin manyan mabobi na kungiyar sun hadu a birnin Istanbul domin rattaba hannu da amincewa da wannan kudiri.
Babban abin takaici ne yadda wasu daga cikin malaman addinin muslunci a wasu daga cikin kasashe suka zama masu yin amfani da sunan addini wajen wanke kwakwalen matasa, tare da ingiza su zuwa ga ayyukan ta’addanci da tashin hankali da sunan muslunci, lamarin da ya bakanta sunan muslunci a duniya.
An gudana r zama 4 kan wannn batu a biranen Washington, London, Jeneva da kuma Doha.
3309922