Kamfanin dillancin labaran Iqna ya habarta cewa, Mohammad Mansur Koshesh babban jami’I mai kula da harkokin yada labarai na ma’aikatar kula da harkokin al’adu na jamhuriyar muslunci ya bayyana cewa, wadannan yan jarida da masu daukar hotuna suna aiki ne a karkashin kafofin yada labarai guda 26 na kasashen ketare, kuma daga kasashe 17, kuma duk za su halarci taron na rasuwar Imam Khomeini (RA) domin daukar labarai da bayanai kan taron baki daya.
Ya kara da cewa kasashen su ne Japan, England, Turkiya, Amurka, UAE, Lebanon, Iraki, Qatar, Kuwait, Afghanistan, Colombia, China, Luxumburg, Italia, Sweeden, Jamus, da kuma Switzerland su ne kasashe 17 da yan jarida za su halarci taron na 14 ga Khordad a kasar Iran.
3310029