IQNA

‘Yan ta’addan Boko Haram Sun kai Hari A Cikin Kasuwa A Arewacin Nigeria

23:53 - June 03, 2015
Lambar Labari: 3310847
Bangaren kasa da kasa, yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kai wania cikin wata kasuwa a garin Maiduguri da ake arewaso gabacin Najeriya wanda ya yi sanadiyyar mutuwa da jikkatar mutane da dama.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gioz na Sky News cewa, a jiya yan ta’addan kungiyar Boko Haram sun kai wania  cikin wata kasuwa a garin Maiduguri da ake arewaso gabacin Najeriya wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 50  da jikkatar wasu mutanen da dama.
Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jahar Borno a tarayar Najeriya na cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu dakamakon harin ta’addancin kungiyar Boko Haram a yau da jikkata suna da daman gaske.
Bayanin ya kara da cewa dan kunar bakin wake ne na kungiyar Boko haram ya tarwatsa kansa a cikin wata kasuwar dabbobi a birnin na Maiduguri da kimanin karfe daya na ranar yau, akalla mutane hamsin sun rasa rayukansu wasu kuma sun samu munan raunuka, kuma akwai yiwuwar adadin wadanda suka rasa rayukan nasu ya karu.

 

Wannan harin ta’addanci na Boko Haram dai ya zo ne bayan kai wasu hare-haren da makaman roka da suka yi da jijjifin safiyar yau a kan birnin na Maiduguri, haka nan ma a ranar Asabar da ta gabata wani dan ta’adda daga kungiyar ya tarwatsa kansa a cikin masallaci a tsakiyar masallata, inda ya kashe mutane fiye da ashirin tare da jikkata wasu da dama.

Sabon shugaban na Najeriya Muhamamd Buhari dai ya sha alwashin mayar da hankali kan wannan matsala ta Boko Haram, domin murkushe su.
3310768

Abubuwan Da Ya Shafa: najeriya
captcha